Boko Haram sun kashe dubban mutane a Baga

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar Boko Haram suna cigaba da kai hare-hare a arewa maso gabashin Nigeria

Hukumomi a jihar Borno sun yi ikirarin cewa 'yan Boko Haram sun hallaka dubban mutane a hare-haren da suka kai a Baga.

Sanata Ma'aji Lawan, wanda ke wakiltar yankin arewacin jihar Borno shi ne ya sheda wa BBC haka.

"Yanzu Baga an gama komai da komai an kone garin. Mutane basu ga 'yan uwansu ba", in ji shugaban karamar hukumar Kukawa da shi ma muka yi hira da shi.

Wasu dubun-dubatar mutanen sun auka cikin kasar Chadi don gudun hijira.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An kone daukacin garin

Bayanai sun nuna cewar daukacin kananan hukumomin da ke arewacin Borno suna karkashin ikon Boko Haram ne.

Bukar ya kara da cewa "Garuruwan karamar hukumar Kukuwa duk a yanzu suna hannun 'yan Boko Haram, kamar su Baga, da Doron Baga, da Dabar Masara, da Mile 4, da Mile 3, da Fish dam da dai sauransu".

A makon da ya wuce ne 'yan Boko Haram suka ci karfin Baga da wasu kauyukan da ke kewaye da garin, inda suka kafa tutocinsu.