Ukraine ta zargi Rasha da yiwa Jamus kutse

Ukraine Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rasha ce ta yiwa Jamus kutse, in ji Arseny Yatsenyuk

Firai ministan Ukraine, Arseny Yatsenyuk, ya zargi Rasha da yin kutse a shafin intanet din Jamus.

Bayanai sun ce kutsen wanda aka zargi jami'an fararen kaya na Rasha da gudanarwa, ya maida hankali ne kan shafin intanet din Merkel da na Majalisar kasar.

Tuni dai wasu masu goyon bayan Rasha kokuma 'yan aware suka dauki alhakin gudanar da kutsen.

Ana kuma kiran gungun mutanen da suna Cyberkut

Ukraine ta yi ikrarin cewa Rasha na da masaniya game da kutsen.

Firai minista Yatsenyuk ya yi zargin ne gabanin wani zama da za su yi da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a yau juma'a.

Sai dai duk da wannan zargi, wani masani ya kalubalanci Ukraine, yana mai cewa babu kwakkwarar hujja da Ukraine da za ta iya gabatarwa kan zargin.

"Ina baiwa jami'an fararen kaya na Rasha shawara da su daina kashe kudaden masu biyan haraji akan ayyukan kutse." In ji Yatsenyuk.