An yi wa Abu Hamza daurin rai da rai

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin daurin rai da rai akan malamin nan mai tsattsauran ra'ayi Abu Hamza bisa samunsa da laifukan ta'addanci.

A watan Mayu ne wata kotu a birnin New York ta same shi da laifukan da suka hada da shirin kafa sansani horar da 'yan ta'adda a Amurkar.

Shara'ar tasa ta biyo bayan tusa keyar sa ne da jami'an Birtaniya suka yi zuwa Amurka. Sai dai a lokacin yanke masa hukunci lauyoyin sa sun roki kotun data yi la'akari da na nakasar sa -- shi mai ido daya ne kuma duka hannayen sa biyu suna guntule.

Sun kuma ce kai shi babban gidan yarin Colarado, wanda yake cike da wadanda su ka aikata muggan laifuka zai saba ka'idojin da aka shimfida kafun a mika shi ga Amurka.

Ainihin sunan sa Mustafa Kamel Mustafa, kuma cikin wasu laifukan da aka tabbatar akan sa harda hannu a wani yunkurin sace masu yawon bude ido daga kasashen yammacin duniya a kasar Yeman a shekarar 1998.