Soji sun ce sun kai hari don kwato Baga

Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar sojin Najeria ta ce ta kai hare-hare ta sama akan 'yan bindigar da suka kwace garin Baga, a jihar Borno dake arewacin Najeria.

Wani mai magana da yawun hukumomin tsaron kasar, Mista Mike Omeri, ya ce tun bayan harin ne aka tura dakaru da kuma kayan fada domin kwato garin.

"Sojoji nata farautar 'yan bindigar tun bayan harin," a cewar Mista Omeri.

Ya kuma kara da cewa jiragen yakin kasar sun kaddamar da hare-hare ta sama akan garin a yunkurin kwato shi.

A ranar asabar data gabata ne wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kaddamar da hari akan garin Baga wanda yake kusa da tafkin Chadi.

Sun fatattaki sojojin da aka girke a garin, sun kuma hallaka mutanen garin da dama.

Har yanzu dai ba'a san adadin mamatan ba.

Sai dai shugaban karamar hukumar Kukawa a Jihar ta Borno ya shaida BBC cewa yawan mutanen zai iya kaiwa "dubu biyu."

Amma dai babu wata kafa data tabbatar da labarin.

Dubban 'yan garin ne suka tsallaka iyaka zuwa kasashe masu makwabtaka da garin.