An kirkiro shirin wasan karta na Komputa

Komputa Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Komputa

Masana kimiyya sun kirkiro wani shiri na Komputa da suka ce ba ya kuskure a wasan karta.

Wadanda suka bullo da shirin sun gaya ma mujallar kimiyya cewar sun magance matsalar da a kan samu ta coge.

Hanyar tafiyar da shirin tana da salo da ya kan kai dab da duk wata hanya mafi inganci "ba za a iya doke ta ba a duk wani wasa na karta."

Kartar da aka gwada wannan shiri da ita an sanya ta a Internet ga mutanen da suke so su gwada ko su kure shirin ko kuma su yi wasan da za su doke shi.

Tun lokacinda masana kimiyya suka fara kokarin kirkirar wannan hanyar ta amfani da kwakwalwa, akwai jerin abubuwan da aka yi wurinda lissafin na Komputa ya bullo da hanyoyin da suka zarce irin yadda mutane ke wasan kartar.

A shekarar 1997 alal misali, wani shiri na kamfanin Komputa IBM da ake kira Deep Blue ya doke Gary Kasparov mutumin da ya fi kowa kwarewa a fagen wasan karta.

To amma wannan nasarar ta na'ura mai kwakwalwa sai da aka sheida ma mutane yadda wasan zai kasance kafin a zartas da hukunci.

Wannan dai ba haka lamarin yake ba a Poker, wurinda mutanen da za su yi wasan ba su da masaniya game da katunan da sauran masu wasan za su yi amfani da su.

Wannan sabon shirin na wasan karta ya sanar da kansa yadda zai kauce ma samun matsaloli.

Naurar ta yi wasan kartar bila-adadin, an kuma shirya wannan shiri ya koyi nadama daga kuskure tare da tunawa da duk wani hukuncin da ba zai kai shi ga samun nasara ba.

Karin bayani