Boko Haram ta sake aukawa Damaturu

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram

Rahotanni daga Damaturu babban birnin Jihar Yobe da ke arewacin Nijeriya sun ce wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sake auka wa garin.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce mayakan na Boko Haram sun shiga birnin na Damaturu ne bayan faduwar rana a jiyan.

Bayan shigar ta su ne wasu mazauna birnin suka ce aka shiga musayar wuta tsakaninsu da sojoji.

Wannan dai shine hari na biyu da a baya-bayan nan 'yan Boko Haram din suka kai a birnin na Damaturu.

A farkon watan jiya ma sun yi wani yukuri na kame birnin, amma sojojin suka fatattake su.

Karin bayani