Dubban Faransawa sun yi maci

Hakkin mallakar hoto EPA

Dubban mutane sunyi maci a birnin Toulose na Faransa domin nuna jimamin su akan hare-haren tada'ddancin da kasar ta ganin a kwanaki ukkun da suka wuce.

Jamai'an kasar kuma na cigaba da girke 'yan sanda a Paris, babban birnin kasar saboda wani babban macin da aka shirya yi a gobe lahadi domin yin Allah wadai da ta'addanci.

Sama da mutane dubu 80 ne suka yi macin a birnin na Talouse.

Wassun sun daga alkalami sama domin nuna alamar tirciya ga duk wani yunkunin dakile fadin albarkacin baki.

Jami'an kasar sun ce sun tsaurara matakan tsaro donmin ganin cewa macin da aka shirya yi gobe na yin Allah wadai da hare-haren ya tafi lafiya.

Patrick Klugman mataimakin magajin birnin na Paris Ya ce "birnin na cikin matukar kaduwa".

Cikin dakarun da aka tura harda 'yan bindiga dadi da aka girke a saman gine-gine.

A birnin na Paris kuma, har yanzu 'yan sanda na cigaba da farautar wasu da suka taimakawa wadanda aka kashe a jiya juma'a.

Cikin su harda Hayat Boumiddine, wadda take tare Amedy Coulibaly, mutumin nan da ya yi garkuwa da wasu mutuane a wani kantin yahudawa.

An ce tana tareda Coulibaly, lokacinda ya kashe wata 'yar sanda ranar Alhamis.

A daya bangaren kuma bayanai na kara fitowa akan garkuwar da aka ce Couliably yayi da mutane a kantin Yahudawan..inda aka ce wani musulmin da ke aiki a kantin ya bowe mutane 15 lokacinda lamarin ya faru.