An yake wa Abu Hamza daurin rai da rai

Abu Hamza
Image caption Abu Hamza

A shekarar 2012 ne Birtaniya ta mika malamin ga hukumomin Amurka bayan doguwar shari'a kuma a bara kotu ta same shi da laifuka da dama da suka hada da yunkurin yin garkuwa da turawa 'yan kasashen yamma a Yemen. Alkalin yace Abu Hamza ya cusawa wasu ra'ayi su kashe wadanda ba musulmi ba a matsayin wani aikin ibada, yana mai cewa har yanzu malamin yana da hadari ga al'umma.

Ya yi suna musamman a kan kalamai masu zafi da yake furtawa a wa'azinsa a wani masallaci a London