Hare- haren ta'addanci ba su kare ba - Hollande

France Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hollande ya ce har yanzu akwai sauran aiki a gaba

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya yi gargadin cewa barazanar da 'yan ta'adda ke wa kasar bai kare ba.

A wani jawabi da ya yi ta kafar talbijin, Mr Hollande ya yi kira ga 'yan kasar da su kasance masu sa ido akan abubuwa da ke faruwa a kusa da su tare da nuna hadin kai.

Mr. Hollande ya kuma jinjinawa kwarewar da jami'an tsaron suka nuna a lokacin samamen.

Gabanin kashe 'yan bindigan, wani gidan talbijin da ya yi magana da su, ya ruwaito cewa 'yan bindigar sun ce sun kai harin ne a madadin reshen kungiyar Al Qaeda dake kasar Yemen.