Jonathan ya zama inuwar 'giginya'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 31 ga watan Disemba ne aka sace yara da matasa 40 a jihar Borno.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya yi tur da harin da aka kai a ofishin mujallar Charlie Hebdo ta Faransa, inda aka kashe mutane 12.

Sai dai shugaban ya yi shiru game da hare-haren da aka kai a arewacin kasar tun daga farkon wannan shekarar.

A wata sanarwa da kakakin shugaban, Rueben Abati ya fitar, ya ce shugaban bai ji dadin harin da aka kai a ofishin mujallar ba.

Ya taya gwamnatin Faransa da 'yan kasar alhinin kisan da aka yi wa 'yan jaridar.

A bangare guda, har yanzu shugaban bai ce komai ba duk da hare-haren da aka kai a jihohin Gombe da Yobe da Borno tun daga ranar daya ga wannan watan, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da dama.

Wasu jami'ai a Borno, sun shaida wa BBC cewa a garin Baga kawai an kashe fiye da mutane da dama a harin da 'yan Boko Haram suka kai a farkon mako.

A ranar 31 ga watan Disamba ne aka sace yara da matasa 40 a jihar Borno.