Ba mu da labarin za a kai hari a Baga - Niger

Garin Baga Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garin Baga

A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin kasar ta musunta cewa tana da labarin 'yan kungiyar Boko Haram za su kai hari a Baga, shi ya sa ta janye sojojinta daga can.

Ministan harkokin wajen kasar Mohamed Bazoum, ya ce matakin janye sojojin da Nijar ta dauka, na da nasaba da alamomin dagulewar al'amurra a yankin.

Inda ya kara da cewa sun ga al'amuran sun dagule ne tun bayan da 'yan Boko Haram suka karbe iko da garin Malam-fatori a cikin watan oktobar da ya gabata.

A ranar Asabar da ya wuce ne dai 'yan Boko Haram suka karfe iko da sansanin sojin hadin guiwa, inda a da sojin na Nijar suke a garin na Baga.

Karin bayani