Nigeria:Kun karbi katin zabe kuwa?

Image caption Hukumar zaben ta ce tana kokari domin tabbatar da cewa kowa ya samu katin zabe

A Najeriya, a yayin da ya rage makonni biyar a gudanar da zaben shugaban kasar, har yanzu wasu 'yan kasar na ci gaba da korafin rashin karbar katin zabe.

Mutanen da BBC ta yi hira da su sun ce kodayake wasu sun karbi katunan zabensu amma da dama ba su karba ba.

Da ma dai wasu 'yan kasar sun roki hukumar zabe INEC ta bar su su yi amfani da katunan zabe na wucin-gadi a zabukan da za a yi a watan Fabrairu ganin cewa ba kowa ne ke da katin dindindin ba.

Hukumar zaben dai ta ce duk wanda bai samu katin zabe lokacin da aka rarraba su ba, zai iya zuwa ofishin hukumar da ke karamar hukumarsa domin ya karba.

Masu sharhi dai na ganin cewa har yanzu hukumar zaben kasar ba ta shirya sosai domin gudanar da zabukan da ke tafe ba, kodayake hukumar ta sha musanta hakan.

Wasu kuma na zargin 'yan kasar da kin mayar da hankali domin tabbatarwa sun karbi katin, suna masu cewa maimakon hakan mutane sun tsaya sai korafi kawai suke yi.