Borno: Ba za a raba katin zabe a kananan hukumomi 15 ba

Hakkin mallakar hoto b
Image caption INEC na cigaba da ba raba katunan zabe na din-din-din a wasu sassan kasar.

Shugaban hukumar zabe na jihar Borno, Farfesa Tukur Sa'ad, ya ce za a fara raba katunan zaben na din-din-din ga al'ummar jihar a ranar Asabar.

Sai dai ya ce ba za a raba katunan a kananan hukumomi 15 ba saboda matsalar rashin tsaro.

Farfesa Sa'ad -- wanda ya sanarwa manema labarai hakan a Maiduguri -- ya tabbatar da cewa za a bayar da katin zaben da kuma ci gaba da rijistar mutane a kowane lokaci.

Ya ce, "Mun karbi katunan zabe na dindindin da yawa, amma har yanzu ba a kawo sauran Maiduguri ba; muna fatan karbar sauran kafin a fara rabawa."

Ya kuma danganta abin da ya jawo rashin raba katin a jihar a kan lokaci da rufe hanyoyi da sojoji suka yi tsawon kwanaki 4 a watan Disambar bara.

Shugaban hukumar zabe na jihar ya kara da cewa za a kuntata raba katunan da ci gaban rijistar zaben ne a kananan hukumomi 12, saboda al'amuran 'yan kungiyar Boko Haram da ya shafi kananan hukumomi 15.

"Tunda ba za mu iya tabbatar da tsaron lafiyar ma'aikatan INEC a wadannan kananan hukumomi ba, za mu yi rabon ne kawai a cikin birnin Maiduguri da Jere da Biu da Monguno da Gubio da Magumeri da Mobbar da Kwaya/Kusar da Bayo da Nganzai, Guzamala da kuma Shani", In ji Farfesa Sa'ad

Da yake bayanin kan batun 'yan gudun hijira kuwa, shugaban cewa yayi za su iya karban nasu katunan ko da a ranar zabe ne.

A hannu guda kuma a ranar Alhamis ne hukumar zabe ta kasa ta ce akalla 'yan Nigeria miliyan talatin da takwas da dubu dari bakwai ne suka karbi katunan zabensu ya zuwa yanzu.

An bayyana adadin ne a wata sanarwa da ta fito daga hannun mai yada labarai na hukumar Mr. Kayode Idowu, ranar Alhamis, in da yace hakan ya zama kashi 71.35 cikin 54,341,610 na adadin mutanen da sukayi rijista a kasar baki daya.