Za a zane wani marubucin intanet a Saudia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saudi Arabia kasa ce da ke kokarin kiyaye shari'ar musulunci.

Wani marubucin shafin intanet a Saudi Arabia ya sha bulala a bainar jama'a sakamakon cin zarafin addinin musulunci da ya yi.

A bazarar bara ne dai aka yankewa Raif Badawi, wanda ya kaddamar da shafin intanet mai suna cibiyar sadarwa ta masu sassaucin ra'ayi a Saudi wato "Liberal Saudi Network", daurin shekaru goma.

Baya ga haka, za a yi masa bulala dubu daya.

Za a yi masa bulalar ce a Jeddah.

Da farko dai za a yi masa bulala hamsin, sannan a yi masa sauran nan gaba kadan.

Amurka ta soki gwamnatin kasar kan hakan, amma duk da haka hukumomi sun ce sai sun yi masa dukkan bulalar.