Sarkin Zazzau ya cika shekaru 40 yana mulki

Sarkin Zazzau
Image caption Sarkin Zazzau

A wannan makon ne ake bikin cikar mai martaba Sarkin Zazzau shekaru 40 a kan gadon sarauta.

Wani babban kalubale da arewacin Nigeria ke fuskanta a yanzu shi ne na rashin tsaro da sarkin na Zazzau Alhaji Shehu Idris ke cewa yana da nasaba da yadda aka karbe al'amurran tsaro daga sarakuna.

To sai dai Sarkin ya ce hanyar kawo karshen matsalar ita ce ta sauraron duk wani mai korafi da kuma duba koke-koken sa.

Ya yi kira ga 'yan kasar da su ci gaba da yin addua'a da nufin neman tsari daga hare-haren 'yan Boko Haram.

Karin bayani