An fatattaki 'yan Boko Haram a Damaturu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption boko haram a damaturu

Rahotanni daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe, a arewacin Najeriya, na nuna cewa hankalin jama'a ya fara dawowa bayan kwashe sa'oi da aka yi a na musayar wuta a daren Juma'a tsakanin wasu da ake ganin 'yan Boko Haram ne da sojoji.

Wani mazaunin garin na Damaturu ya bayyana wa BBC cewa wannan karon 'yan Boko Haram din ba su ji da dadi ba a hannun sojojin.

Mutumin ya ce an wayi gari an ga alamun alburusai a kan tituna da gine-gine sannan kuma sojoji sun kashe 'yan kungiyar da dama.

Sai dai kuma mutumin ya sheda wa BBC cewa 'yan kungiyar sun kona wani rukunin shaguna da wani babban ofishin 'yan sanda da kuma wani babban masallaci, kafin daga bisani a fatattake su.

Haka kuma an ce wani kaftin din soji ya rasa ransa sakamakon fafatawar.

Kawo yanzu, hukumomin Najeriyar ba su ce komai ba dangane da al'amarin.