Za a yi maci na bijere ma ta'addanci

Gangamin nuna adawa ga ta'addanci Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Gangamin nuna adawa ga ta'addanci

Mutane sama da miliyan daya ne ake sa ran za su halarci wani maci da za a yi na ratsa birnin Paris nan gaba a yau a wani gagarumin gangami na nuna goyon baya ga yaki da ta'addanci.

An kira taron ne don nuna adawa ga hare-haren da aka kai 'yan kwanakin nan, inda wasu masu kaifin kishin Islama suka kashe mutane goma sha-bakwai.

Daga cikin Shugabannin kasashen da suka shirya shiga wannan gangami har da Prime Ministan Brittaniya David Cameron da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Prime ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu.

Karin bayani