An fara kokawa da aikin raba kati a Borno

Nigeria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu 'yan jihar Borno sun fara kokawa da ayyukan ba da katin zabe na din-din-din

A jahar Borno da ke arewacin Najeriya an fara rarraba katunan zabe na din-din-din ga jama'ar jahar.

Za kuma a kwashe 'yan kwanakin nan masu zuwa ne ana gudanar da aikin ba da katin.

Sai dai a yayin da ake cewa an soma ba da katin, tuni dai wasu mazaunan garin Maiduguri babban birnin jahar ta Borno suka fara korafin cewa ba su ga inda aka manna sunayensu ba ballantana su je su karbi nasu.

Hakan na faruwa ne yayin da aka kai wani hari bam a wata kasuwa dake Maiduguri wanda ya hallaka mutane 19.

Hukumar 'yan sandan jahar sun ce bam din ya tashi ne a jikin wata yarina mai shekaru 10.

Kuma a cewar wadanda suka shaida harin, ga dukkan alamu yarinyar ba ta da masaniyar cewa bam ta ke dauke da shi.