Za a zaftare albashin 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yawan albashin 'yan majalisar dokokin Burkina Fasa ya haifar da zazzafar mahawara

'Yan majalisar dokokin Burkina Faso sun yanke shawarar zaftare rabin albashinsu daga fiye da dala dubu 3 a kowanne wata.

Hakan ya biyo bayan zazzafar mahawara da mutanen kasar suka yi ta yi ne a shafukan sada zumunta na intanet bayan an samu labarin albashin da 'yan majalisar ke barba.

Albashin da bai wuce ka'ida ba da ake biyan ma'aikata Burkina Faso, shi ne kimanin dala 150 a wata.

Wani daga cikin 'yan majalisar ya ce albashin nasu ya kunshi alawus na zaman majalisa, da na aikce-aikacen ofis, dana kula da lafiyar su, da kuma kudin sayan man fetur.

Sai dai a ganin babban jami'in kungiyar Balai Citoyen, Mista Herve Kam bai kamata a rika biyan 'yan majalisar kudin zaman mahawara da suke ba.

Tun a watan Oktoban bara lokacin da aka tilasta wa Shugaba Blaise Compore sauka daga mulki, aka kafa kwamitin gwamnatin riko wanda ke da mutane 90, domin maye gurbin majalisar dokokin kasar.