An daure dalibin da ya ce babu Allah

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kundin tsarin mulkin Masar ya haramta aibanta addinin musulunci da na kirista

A kasar Masar, an yanke wa wani dalibi hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda ya nuna bai yi imani akwai Allah ba a shafinsa na Facebook.

Lauyan Karim al-Banna, ya ce an kuma samu dalibin da laifin aibanta addinin musulunci.

Mahaifin dalibin bai goyi bayansa ba a kotu, inda ya ce yaron nasa, yana daukar wasu tsauraran akidoji da suka sabawa musulunci.

Za a iya jingine hukuncin daurin idan dalibin ya biya tarar dala 140, kafin a saurari hukuncin kotun daukaka a watan Maris.

Kundin tsarin mulkin kasar Masar ya haramta aibanta addinan da kasar ta amince da su ba, wadanda suka hada da addinin musulunci da na kirista.