Jonathan yana soki-burutsu - Fashola

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fashola ya ce Jonathan ya gaza

Gwamnan jihar Lagos da ke kudancin Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce shugaban Najeriya ba shi da abin da zai gaya wa 'yan kasar don su sake zabensa shi yasa yake soki-burutsu.

A wani dogon sharhi da ya rubuta a jaridar ThisDay, gwamna Fashola ya ce maimakon Mr Jonathan ya gaya wa 'yan kasar dalilan da suka sa ya kasa ceto 'yan matan Chibok da kuma yadda har yanzu bai fitar da rahoto kan kudi $12bn da tsohon shugaban babban bankin kasar ya ce kamfanin man fetur bai saka a asusunsa ba, shugaban ya mayar da akalar kamfe dinsa kan abubuwan da ba su da muhimmanci.

Gwamna Fashola ya ce ya yi mamakin cewa duk da zuwan da shugaba Jonathan ya yi Lagos don bude yakin neman zabensa, bai gaya wa 'yan kasar komai ba game da yadda zai kare rayukansu, musamman ganin cewa 'yan Boko Haram sai fadada hare-harensu suke yi.

Mr Fashola ya kara da cewa shugaba Jonathan bai cika alkawuran da ya yi 'yan kasar ba don haka bai ga dalilin da zai sa a sake zabensa ba.

Jam'iyyar PDP mai mulkin kasar dai ta ce shugaban ya kawo sauye-sauye a rayuwar 'yan kasar saboda haka ne ma take so a sake zabensa.