Kofi Annan zai fara ziyara a Nigeria

Mr Kofi Annan Hakkin mallakar hoto
Image caption Tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr Kofi Annan

Tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr Kofi Annan zai fara wata ziyara ta kwanaki biyu a Najeriya.

A yayin ziyarar ta sa Mr Annan zai kasance babban mai jawabi a taron da za a yi da masu ruwa da tsaki a harkokin zaben Najeriyar a Abuja, a matsayin shugaban cibiyar kula da zabuka da demukradiyya da kuma tsaro ta duniya.

Ana sa ran tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniyar wanda kuma shi ne shugaban cibiyar Annan, mai rajin tabbatar da zabe cikin gaskiya da adalci zai gana da wasu kungiyoyin farar hula na kasar.

A wata hira da BBC shugaban cibiyar wanzar da ci gaba da kuma demukradiyya a Najeriya Dr Kole Shettima ya ce ziyarar ta Kofi Anan tana da tasiri wajen tabbar da ganin hukumomin Nigeria sun gudanar da sahihin zabe a watan Fabrairu.