Janar Olukolade ya ce mutane 150 aka kashe a Baga

Birgediya Janar Olukolade Hakkin mallakar hoto
Image caption Birgediya Janar Olukolade

Rundunar sojan Nijeriya ta karyata adadin mutanen da ake zargin an kashe sakamakon da harin da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai a garin Baga na jihar Borno a kwanakin baya.

Duk da cewa hukumomin sojin sun tabbatar da kai hare-haren, amma sun ce adadin wadanda suka mutun , dari da hamsin ne, ba dubu biyu ba, kamar yadda wasu rahotanni ke cewa .

Hakan na kunshe ne cikin wata hira da manema labaru da shugaban cibiyar bada bayanai kan harkokin tsaro ta kasa, Manjo Janar Chris Olukolade ya yi .

Janar Kolade ya ce mutane da dama sun bar garin Baga, kafin harin 'yan kungiyar.