An soki gangamin da aka yi a Faransa

Shugaba Muhammadu Issufou na Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Muhammadu Issufou na Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, ana ci gaba da cece kuce dangane da gayyatar da hukumomin kasar Faransa suka yi wa wasu shugabannin Afrika na halartar jerin gwanon da kasar ta shirya domin yaki da ta'addanci.

Wasu malaman addinin Musulunci da 'yan siyasa daga bangaren adawa sun yi Allah wadai da halartar gangamin da suka ce ya saba ma akidar addinin musulunci.

Sai dai a nata bangaren jam'iyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar ta ce bata ga aibun halartar gangamin da wasu shugabannin Afrika suka yi ba ciki har da shugaban Nijar Muhammadu Issufou.

Fiye da mutane miliyan daya da rabi ne wadanda suka hada shugabannin kasashen duniya 40 suka yi tattaki a birnin Paris da wa su biranen kasar Faransa a ranar Lahadi don nuna hadin kan kasa, bayan hare-haren da 'yan bindiga suka kai a cibiyar mujallar Charlie Hebdo da ke Paris.