An sake bude makarantu a Peshawar

Hakkin mallakar hoto afp getty
Image caption Harin 'yan Taliban a wata makaranta ya halaka mutane 140

An tsaurara matakan tsaro a birnin Peshawar na kasar Pakistan yayin da dalibai da malamai ke komawa makaranta a karon farko tun bayan 'yan Taliban sun hallaka fiye da mutane 140 a wata makaranta.

An dai gudanar da wani buki don tunawa da wadanda suka rasu a harin.

Daya daga cikin malaman makarantar da aka kai harin Andaleeb Aftab wacce ta rasa danta ta bayyana lokacin da ta ga 'yan makaranta na guje guje lokacin da harin:

Rahotanni sun ce daukacin makarantu a lardin Khyber Pakhtunkhwa sun bude bayan karin hutun da suka yi saboda harin.

A 'yan watannin nan gwamnatin Pakistan ta dawo da zartar da hukuncin kisa a kasar, yayin da ake yunkurin kafa kotunan soji don gurfanar da masu aikata laifuffukan ta'adanci.