An gano baraka a manhajar Android

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kashi 60 cikin dari na masu amfani da wayoyin Android, suna amfani ne da tsohuwar manhaja

Miliyoyin masu amfani da wayoyin Android za su iya fuskantar matsala da wayoyinsu saboda kamfanin Google ya rage sabunta manhajojin tsaro na wayoyi masu amfani da tsohuwar manhajar Android.

Matsalar za ta shafi kimanin kashi 60 cikin dari na masu amfani da wayoyin Android 4.3 ko kuma kasa da haka.

Masu bincike wadanda suka gano wannan sauyi sun ce wannan labari zai yi wa batagarin mutane dadi.

Masu binciken sun gano za a fuskanci hadari sosai wajen bude shafin intanet na wayoyin Android 4.3 Jelly Bean.

A cikin shekarar da ta gabata, masu bincike, Tod Beardsley da Joe Vennix na kamfanin Rapid7 sun gano hadura 11 da za a iya fuskanta wajen bude shafin intanet.

Mista Beardsley ya ga azancin kamfanin Google na daukar wannan mataki, domin kuwa kashi 60 cikin dari na masu amfani da wayoyin Android ne masu tsohuwar manhaja.

"Yanzu haka za a iya cewa fiye da wayoyin Android miliyan 930 ne kamfanin Google ba ya sabunta manhajojin tsaron su" inji Beardsley.

Kakakin kamfanin Google ya ki ya ce uffan a game da sauyin tsare-tsaren nasu.