'Yan gudun hijirar Baga 5,000 sun isa Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A farkon wannan watan ne 'yan kungiyar Boko Haram suka karbe iko da garin na Baga

Kungiyar agajin likitoci ta MSF ta ce yana da wuya ta iya kai wa ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa-maso-gabashin Nigeria domin yanki yana cike da hatsari.

Kungiyar ta ce kimanin mutane 5,000 ne suka samu tserewa daga garin Baga kuma suka isa Maiduguri, bayan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai garin.

Kuma mafi yawancin 'yan gudun hijirar mata ne da kananan yara, yayin da kwanaki goma bayan kai harin fararen hula na ci gaba da neman tudun mun tsira.

Sannan wasu dubban da suka tserewa rikicin Baga da suka nufi kasar Chadi ke ci gaba da kasancewa a wurare masu hatsari da kuma rashin hanyoyin da motoci za su iya bi.

Wata jami'ar kungiyar likitocin, Isabelle Mouniaman ta shaida wa BBC cewa a halin yanzu kimanin 'yan gudun hijira 500,000 ne a birnin Maiduguri.