Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Biu

Image caption A wannan karon 'yan Boko Haram sun sha kashi

Rundunar sojin Nigeria ta tabbatar da cewa ta dakile wani hari da 'yan Boko Haram suka kaddamar da garin Biu na jihar Borno.

Kakakin rundunar, Chris Olukolade ya shaida wa BBC cewar rundunar ta yi nasarar fatattakar 'yan Boko Haram tare da damke mayakan kungiyar su biyar da kuma motocinsu.

Wani mazaunin garin a hirarsa da BBC ya ce an kashe 'yan Boko Haram shida a lamarin, sannan mota daya tal ta 'yan Boko Haram aka ga ta koma sansaninsu daga cikin motocin 11 da aka ga sun nufi garin Biu da safiyar ranar Laraba.

"Da misalin karfe 7 muka fara cikin karar harbe-harbe daga sai 'yan Boko Haram suka kona caji ofis na 'yan sanda", in ji wani dan Biu.

Ya kara da cewa "Sojoji da 'yan civilian JTF suka hana su (Boko Haram) shiga Biu sannan aka ci karfin 'yan Boko Haram, kuma na ga gawawwakin 'yan Boko Haram a kan wasu hanyoyi".

Bayanai sun nuna cewa garin Biu shi ne kadai gari a yankin kudancin Borno da ba ya karkashin ikon 'yan Boko Haram.