Kamaru ta kashe 'yan Boko Haram 143

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kashe sojin Kamaru guda daya, in ji Ministan kasar.

Gwamnatin Kamatu ta ce ta kashe 'yan Boko Haram 143 lokacin da suka kai hari a sansanin dakarun tsaro da ake kira BER, a takaice, a garin Kolofata wanda ke kan iyakar Kamaru da Najeriya.

A wata sanarwa da kakakin gwamnatin, Minista Issa Tchiroma Bakary ya fitar, ya ce sojin kasar guda daya ya mutu a gumurzu da Boko Haram, sannan guda hudu suka jikkata.

Rahotanni sun ce bangarorin biyu sun kwashe sama da sa'o'i biyar suna yin musayar harbe-harbe bayan dirar mikiyar da maharan suka yi a yunkurin kwace barikin sojojin na Kolofata.

A wannan gari na Kolofata ne, a bara kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da uwar gidan Mataimakin Firaminista Amadou Ali, da kuma wani basarake.