Bam ya fashe a garin Gombe

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption A bara bam ya fashe a tashar motoci a Gombe

Rahotanni daga Gombe sun ce wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a unguwar 'kasuwar mata' da ke tsakiyar birnin.

Lamarin ya auku ne a kusa da sansanin jami'an tsaro da aka fi sani da 'anti kalare', wanda ba shi da tazara sosai daga jam'iar jihar Gombe.

Bayanai sun ce bam din ya fashe ne gabda lokacin Sallar Magariba.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai a kan adadin wadanda lamarin ya rutsa da su.

A karshen watan Disamba ma mutane a kalla 20 ne suka rasu sannan fiye da 40 suka jikkata sakamakon tashin bam a wata tashar mota a Gombe.

A cikin 'yan kwanakin nan kungiyar Boko Haram ta tsananta kai hare-hare a jihohin arewa maso gabashin kasar.