An fitar da sunayen masu zaben bana a Nigeria

Farfesa Jega
Image caption Farfesa Jega

Hukumar zabe a Nigeria, ta mika kundin rajistar masu kada kuri'a na kasar ga wakilan jam'iyyun siyasar.

Kundin rajistar na kunshe ne da adadin 'yan kasar da suka yi rajista domin kada kuri'a a zaben da za a gudanar a wata mai zuwa.

Hukumar ta ce a yanzu mutane miliyan sittin da takwas ne ta tantance domin kada kuri'a, kasa da miliyan saba'in da uku da ta yi wa rajista a zaben a 2011.

Shugaban hukumar zaben, Farfesa Attahiru Jega ya bada tabbacin cewa za a yi zabe a duk fadin kasa, matukar akwai matakan tsaro.