Annan ya nuna fargaba kan zaben Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Annan ya ce rashin bai wa kowa da kowa damar yin zabe zai iya shafan kyawun zabe a Nigeria

Tsohon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Mista Kofi Annan, ya nuna fargaba game da yiwuwar zabe a Najeriya saboda tabarbarewar matsalar tsaro.

Mista Annan -- wanda ya kai ziyara a kasar -- ya shaidawa BBC cewa gudanar da zabe a watan Fabrairu cikin kwanciyar hankali abu mai muhimmanci ga kasar da ma Africa baki daya.

Ziyarar ta sa ta zo ne a daidai lokacin da wasu ke fargabar za a iya samun rikice-rikicen da suka shafi zabe, da kuma illolin da za su haifar ga makomar kasar.

Mista Annan ya ce kowanne dan Najeriya yana da gagarumar gudunmuwa wajen tabbatar da an gudanar da zabe na gaskiya, cikin kwaciyar hankali da lumana.

Ya ce duk da rikice-rikicen Boko Haram, akwai bukatar hukumomi a kasar su dauki matakan bai wa kowa da kowa damar kada kuri'a a zaben domin ya yi kyau.