Boko Haram: Chadi ta rufe iyakarta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijira ne suka tsallak cikin Chadi daga Najeriya.

Rahotanni daga kasar Chadi na cewa an rufe iyakar kasar da Najeriya na wucin gadi sakamakon hare-haren Boko Haram.

Rahotannin na cewa gwamnatin kasar ta sanya dakarunta cikin shirin ko-ta-kwana domin mayar da martani kan yiwuwar samun hare-hare daga kungiyar ta Boko Haram.

Kazalika, gwamnatin ta Chadi tana daukar matakin tsugunar da 'yan gudun hijrar da suka tsallaka cikin kasar daga Najeriya.

A kwanakin baya ne dai Firai Ministan kasar ya ce fiye da 'yan gudun hijira 13,000 ne suka shiga kasar daga Najeriya, yana mai yin kira ga kasashen duniya su tallafa musu.

Da dama daga cikin 'yan gudun hijirar dai sun tsere ne daga garin Baga da 'yan Boko Haram suka mamaye kwanakin baya.

Najeriya da kasar Chadi ba su da iyaka ta tsandaurin kasa sai dai ta ruwa wato tafkin Chadi.