Charlie Hebdo: Shekau ya yi murna

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta ce kaddamar da jihadi a Nigeria

Kungiyar Boko Haram a Nigeria ta ce tana Allah wadai da wallafa zanen batanci ga Annabi Muhammadu da jaridar Charlie Habdo ta yi a kasar Faransa.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafin intanet na Youtube, shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya ce suna farin ciki da harin da aka kaiwa ofishin mujallar da ta wallafa zanen.

Shekau ya ce "Mun yi farin ciki da abinda ya faru ga al'ummar Faransa na daga azaba, kamar yadda aka zubar da jininsu a cikin kasar su."

Bugun farko na majallar Charlie Hebdo ya fito, bayan harin da 'yan bindiga suka kai kan ofishin mujallar a makon jiya.

Rahotanni sun nuna cewa mujallar ta yi kasuwa, kasancewar an saye ta cikin 'yan sa'o'i kadan, sakamakon yadda mutane suka dinga shiga layi don sayen mujallar.

Masu mujallar dai sun ce za su sake wallafa karin kwafe miliyon biyar.