Paparoma ya yi tir da nuna banbamcin addini

Paparoma Francis Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paparoma Francis

Paparoma Francis ya hori 'yan kasar Sri Lanka da su yi ko yi da kyawawan halayyar Joseph Vaz tare da kokarin magance banbamcin addinin da ke tsakanin su.

Paparoman ya bayyana haka ga dandazon 'yan kasar da suka taru a gabar teku da ke birnin Colombo don yin addu'o'i na musamman inda ya yi tir da nuna bambamcin addini.

Paparoman ya kuma gaisa da wasu talakawa tare da nakasassu lokacin da iso gabar tekun.

Ana saran zai yi tattaki zuwa wani karamin coci da ke wani yanki da aka gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati na 'yan tawayen Tamil a lokacin yakin basasar kasar.