Boko Haram ta yi kaca-kaca da Baga

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amnesty ta ce barnar da aka yi ta fi adadin da gwamnati ta bayar

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce an yi mummunar barna a hare-haren da Boko Haram ta kai Baga da Doron Baga da ke jihar Borno ta Najeriya.

Wasu hotunan da kungiyar ta fitar, wadanda ta dauka daga tauraron dan Adam gabanni da kuma bayan kai hare-haren sun nuna cewa daruruwan mutane ne aka kashe da suka hada da mata masu juna-biyu, da yara da kuma tsofaffi.

Rahoton kungiyar ya ce mutanen da suka mutu sun haura 150 din da rundunar sojin Najeriya ta sanar.

Kungiyar ta ce an lalata gidaje 620 a Baga, sannan aka lalata gidaje 3100 a Doron Baga.

Wakilin kungiyar a Najeriya, Daniel Ere, ya ce 'yan Boko Haram sun kusa shafe daya daga cikin garuruwan biyu daga taswirar duniya, yana mai cewa hare-haren na daga cikin mafi muni tun da Boko Haram ta fara kai hare-hare.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service