Rikicin Boko haram ya shafi kashi 41 na yara

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Mata da kananan yara ne kaso mafi girma a cikin 'yan gudun hijirar da suka tserewa rikicin Boko Haram

Hukumar agajin gaggawa ta Nigeria ta bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a yankin arewacin kasar sun shafi rayuwar kashi 41 cikin dari na kananan yaran da ke yankin.

Jami'in hukumar na arewa maso gabashin kasar, Mohammed Kanar ya tabbatar da cewa kimanin yara kusan 200 ne ba a san inda iyaye ko 'yan uwansu suke ba a sansanoni 'yan gudun hijira daban-daban na jihar Adamawa.

Inda ya kara da cewa kalilan ne daga cikinsu suke tare da makotan da suka sani tun a garuruwansu na asali.

Masana dai sun bayyana cewa irin wadannan rigingimu musamman ma kashe-kashe, kan yi mummunan tasiri a kan rayuwar yara idan ba a dauki matakin kyautata rayuwarsu ba.