Paparoma ya kare 'yancin fadin albarkacin baki

Paparoma Francis Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Paparoma Francis

Fafaroma ya kare 'yancin bayyana albarkacin baki -- to amma ya ce bai dace a tsokani wasu ta hanyar cin zarafin addininsu ba.

Ya bayyana haka ne a lokacin hira da manema labaru a kan hanyarsa ta zuwa kasar Philippines inda yake wata ziyarar kwanaki biyar.

Bayanin na Fafaroma Francis ya biyo bayan harin da aka kai wa mujallar barkwancin nan ta Faransa Charlie Hebdo a Paris cikin makon da ya wuce.

Shugaban kasar Philippines Benigno Aquino da dubun dubatar mutanen dake da cikin annashuwa ne suka yi wa Fafaroman marhabin a Manila.