FBI ta gano yunkurin kai hari a Amurka

Shugaban Amurka Barrack Obama Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama

Jami'an hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI sun kame tare da gurfanar da wani mutum a birnin Ohio da ake zargi da kulla makarkashiyar kai hari a ginin Majalisar dokokin Amurka da ke Washington.

Wasu takardun da aka gabatar a gaban kotu sun ce mutumin mai suna Christopher Cornell, an kama shi ne bayan da yayi yunkurin sayen bindiga da kuma alburusai har guda dari shida.

An kuma yi zargin cewa ya yi ta bincike kan yadda ake harhada bama bamai ta hanyar amfani da batutu.

Jami'an hukumar ta FBI sun ce mutumin da ake zargi ya shirya tada bam ne tare da harbin mutanen da ke aiki a Majalisar dokokin.

Haka kuma an yi zargin cewa ya sanya wasu sakonni a shafin twitter na nuna goyon baya ga mayakan kungiyar IS inda ya rika amfani da sunan Raheel Mahrus Ubaydah.