BBC ta kaddamar da kyautar Komla Dumor

Image caption Margayi Komla Dumor

An bude kofar shiga gasa domin samun kyautar BBC ta Komla Dumor ta bunkasa aikin jarida ga 'yan Afrika masu hazaka daga yanzu har zuwa karfe 23.59 a agogon GMT na ranar Litinin 2 ga watan Fabarairun 2015.

BBC ta kadammar da kyautar ce domin karrama tsohon ma'aikacinta mai gabatar da labaran talabijin Komla Dumor wanda ya rasu a bara yana da shekaru 41 da haihuwa.

Komla hazikin dan jarida ne dan asalin kasar Ghana wanda bai yi tsawon rai ba, amma kuma ya taka rawa a Ghana da Afrika da kuma duniya baki daya a gidan rediyon Joy FM da kuma BBC.

Saboda lakantar aikin jarida, ya iya gabatar da labaran Afrika ga duniya baki daya. BBC ta shirya wannan kyauta ce domin ci gaba da tunawa da Komla.

A yanzu an bude kofa ga masu son shiga gasar kyautar "BBC World News Komla Dumor Award" ga duk wanda ke zaune a Afrika kuma yake aiki a cikin nahiyar kuma yake da kwazo a aikin jarida tare da sannin makamar yadda ake ba da labarai a kan nahiyar, to wannan dama ce ya zama tauraro.

Wanda ya lashe kyautar zai samu damar kara kwarewa da gogewa a kan aikin, tare da ma'aikatan BBC a London na tsawon watanni uku.

Zakaran zai samu damar aiki a talabijin da rediyo da kuma intanet na BBC mai masu sauraro miliyan 265 a fadin duniya.

Editan Afrika na BBC, Solomon Mugera ya ce "Komla fuskar Afrika ne, matashi, mai kwazo da basira. Yana da saukin kai ga murmushi wanda ya san yadda zai ba da labarai a kan Afrika ko masu dadi ko marasa dadi. BBC za ta ci gaba da karrama Komla. Muna neman matashi mai basira wanda zai gaji Komla."

Za a rufe shiga gasar a ranar Litinin, 2 ga watan Fabarairun 2015 da karfe 23.59 a agogon GMT.

Domin karin bayani a kan gasar da sharuddan gasar sai ku ziyarci bbc.com/komladumor.

Kyautar BBC ta Komla Dumor za a bayar ne tare da hadin gwiwar Standard Chartered.