"Ba mu ji dadin ziyarar Jonathan ba"

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a jihar ta Borno

Mazauna jihar Borno sun ce ba su ji dadin ziyarar da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ba.

A hirar da suka yi da BBC, sun ce sun gane cewa shugaban bai damu da su ba, suna masu cewa ya kai ziyarar ce domin yakin neman zabe.

Sun yi tambayar ce me ya sa shugaban bai kai ziyarar ba duk da kashe-kashen da ake yi musu tsawon lokaci, sai yanzu da zabe ya kusa?

Wasu daga cikinsu sun ce ziyarar tasa ba za ta sa su kada masa kuru'a a zaben da ke tafe ba