Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tashin hankalin zabe

Wasu kungiyoyin kare hakkin bil-Adama a Najeriya sun kiyasta cewa fiye da mutane 500 ne suka rasa rayukansu a rikice-rikicen da suka biyo bayan zabukan 2011.

Ko me ke haddasa irin wadanann rikice-rikice?

Wai shin wacce illa wadannan tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe ke haifarwa, kuma me ya kamata a yi don hana aukuwar su?

A birnin Kanon Dabo jama'a sun tafka muhawara a kan wadannan batutuwa, kuma a jerin shirye-shiryenmu na musamman a kan zabukan Najeriya, za mu zo muku da wannan muhawara; sai ku kasance da mu a Filin Ra'ayi Riga na wannan makon.