Kwankwaso ya soki ziyarar Jonathan a Borno.

Shugaba Jonathan na Nijeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Jonathan na Nijeriya

Shugaban Najeriya Goodluck ya kai ziyarar ba-zata jihar Borno, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun bayanai game da mummunar illar da harin 'yan Boko Haram ya yi a garin Baga na jihar.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ke kai ziyara a yankin tun cikin shekara ta dubu biyu da sha uku.

An dai soke ziyarar da shugaban ya shirya kai wa garin Chibok, inda 'yan kungiyar Boko Haram suka sace fiye da 'yan mata 'yan makarantar sakandire dari biyu.

A wannnan ziyarar ta ba-zata, tuni wasu gwamnonin hamayya a Nijeriya suka fara maida martani da sukar Shugaban kasar da gwamnatinsa.

A tattaunawarsu da BBC, gwamnan jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya saba sukar shugaban Goodluck din, ya ce ziyarar tana da nasaba da siyasa, kuma ba yanzu ne ya kamata ya kai ta ba.

Karin bayani