Nijar ta hana sayar da Charlie Hebdo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban na Nijar ya sha suka daga 'yan kasar saboda ziyarar da ya kai Faransa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce kada a kuskura a sayar da mujallar Charlie Hebdo a kasar.

Mujallar dai ita ce ta yi zanen batanci kan annabi Muhammad (SAW).

A wata hira da BBC ta yi da ministan harkokin wajen kasar, Bazoom Mohammed, ya musanta cewa shugaban kasar, Mohammadu Issoufou ya je kasar Faransa ne domin taya shugabanninsu jaje.

Shugaban dai ya bi jerin gwanon da wasu shugabannin duniya 50 suka yi ne a Paris a karshen makon jiya domin nuna goyon baya ga mujallar ta Charlie Hebdo.

Sai dai Nijar ta ce shugaban ya je Faransa ne domin yin Allah wadai da batancin da mujallar ta yi wa annanbi Muhammad(SAW)