Ziyarar mu Paris ta Allah wadai ce - Nijer

Shugaba Issofou na Nijer Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Issofou na Nijer

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kare kan ta daga sukar da ake ma Shugaban kasar bisa wata ziyara da ya kai birnin Paris a daidai lokacin da ake hayaniyar nan ta Charlie Hebdo.

A wata sanarwa da ta fitar, ta yi bayanin dalilan halartar da shugaban kasar ya yi ta jerin gwanon da aka yi a paris karshen makon da ya gabata, tare da yin Allah wadai da jaridar Sharlie.

Har ila yau kuma, a cikin sanarwar, kasar ta Nijar ta yi hani ga sayar da jaridar a cikin kasar ta.

Ministan harkokin wajen kasar Bazoom Mohammed a hirar su da BBC - ya bayyana cewa ziyarar da Shugaba Issofou Muhammadu ya kai birnin na Paris don bayyana wa muhukuntan kasar ne cewar, abinda wasu 'yan tsiraru suka aikata, ba haka musulunci yake ba.

Kazalika kuma ya ce, Nijer din ta janye sojojin ta ne daga Baga don gudun kada 'yan Boko Haram su kassara su.

Karin bayani