Ana zanga-zanga kan zanen batanci a Niger

Image caption Kasashen Musulmi na duniya da dama sun fusata da sabon zanen

Rahotanni daga birnin Zinder a jamhuriyyar Nijar na cewa masu zanga-zanga sun fantsama kan tituna domin nuna adawa da zanen batancin da mujallar Charlie ta yi ga fiyayyen halitta.

Wasu bayanai sun nuna cewa an cinna wa wasu gine-gine wuta ciki har da cibiyar al'adu ta Faransa da ke Zinder.

Haka kuma an kona wani coci-coci a yayin zanga-zangar adawa da abin da mujallar barkwancin ta yi.

A cewar rahotannin dai tuni 'yan sanda suka fara maida martani da harbe-harbe.

A wannan makon ne mujallar Charlie Hebdo ta sake wallafa wasu mujallu dauke da wani zane da ta ce na Manzon Allah (SAW).