An baza soji a titunan kasar Belgium

soji suna sintiri Hakkin mallakar hoto Reuters

Soji suna yin sintiri a titunan kasar Belgium, a karon farko cikin shekaru talatin da biyar, domin tsare wuraren da aka iya kai wa harin ta'addanci.

Inda aka tura sojin ya hada da unguwar Yahudawa, da ofisoshin jakadancin Amurka da na Isra'ila.

Ministan tsaro, Steven Vandeput, ya ce an baza sojin ne domin su kare ofisoshin jakadanci da kuma unguwannin Yahudawa.

Ya ce, "Shawarar tura sojin ita ce don a sami tsaro, domin 'yan sanda su sami yin aikin 'yan sanda na sintiri a tituna da tabbatar cewa komi lafiya."

Sai dai wasu mazauna garin Antwerb sun bayyana rashin gamsuwa da matakin.

Wani mazaunin garin ya ce, "Ina ganin a wannan lamari muna bukatar karin matakan kariya ne ba amfani da karfi. Ka san idan mutane suka ga sojoji akan tituna su kan razana. Saboda haka wannan na iya haifar da matsaloli maimakon samar da mafita."

Masu bincike suna ci gaba da yin tambayoyi ga wasu mutane goma sha uku, an kuma tuhumi wasu guda biyar.