Mutane hudu suka mutu a Damagaram.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption zanga-zanga a Niger kan Charlie Hebdo

A Jumhuriyar Nijer, zaga-zangar nuna kyamar jaridar nan Charlie Hebdo ta Faransa, ta haddasa mutuwar a kalla mutane hudu a birnin Damagaram.

An yi zanga-zangar ne bayan Sallar Jumma'a a jiya, kuma hukumomin kasar sun tabbatar da wannan batu tare da bayyana adadin mutanen da suka jikkata.

Wakiliyar BBC wadda ta zanta da mutane da dama a lokacin da ake zanga-zangar ta ce, jami'an tsaro sun yi amfani da harsasai na gaske a kokarin tarwatsa masu zanga-zangar.

Karin bayani