Paparoma na addu'i'o a birnin Tacloban

Paparoma Francis a lokacin da ya isa kasar Philippine Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paparoma ya kai wannan ziyara ne domin nuna alhini da iftila'in mahaukaciyar guguwar Haiyan da ta fadawa kasar shekara guda da ta wuce.

Paparoma Francis ya jagoranci addu'o'i na musamman a sararrin subahana a birnin Tacloban na kasar Philippine, inda ya fuskanci mummunar guguwar Haiyan wadda ta daidaita birnin shekara guda da ta wuce.

Dubun dubatar mutane, wasu sanye da rigunan ruwa ne suka halarci wurin addu'o'in.

Jama' sun yi ta sowa da yin tafi, a lokacin da Paparoma ya ke cewa yana ganin hotunan yadda mahaukaciyar guguwar Haiyan ta daidaita birni Tacloban, sai ya ji cewa lallai ya kamata ya kawo ziyarar lhini kasar Philippine.

A bangare guda kuma Paparoma Francis zai gana da wasu daga cikin wadanda suka samu tsira daga iftila'in guguwar, da kuma wasu daga cikin iyalan mutane dubu bakwai da suka rasa rayukansu a bala'i mafi muni da ya afkawa kasar.