Ban yarda da Paparoma ba - David Cameron

Prime Ministan Brittaniya Hakkin mallakar hoto
Image caption Prime Ministan Brittaniya

Prime Ministan Burtaniya David Cameron, ya ce bai amince da kalaman da Paparoma Francis ya yi ba kan cewar haramun ne ka ci zarafin addinin wasu.

Da yake maida martani ga harin da masu kaifin kishi Islama suka kai a gidan jaridar Sharlie Hebdo na kasar Faransa, Paparoman ya ce duk wanda ya ci zarafin mahaifiyar wani, to babu shakka sai wanann mutumin ya dauki mataki a kai.

Mr Cameron ya kara da cewar a al'ummar da take da 'yanci, mutum na da 'yancin cin rafin addinin wani.

Ya shaidawa gidan talabijin na CBS na kasar Amurka cewa su ma kafafen yada labarai ya kamata su dinga wallafa abubuwa irin wadannan in dai har suna bin tsarin na 'yancin fadar albarkacin baki.

Karin bayani